Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Jajanta wa Nijar Kan Kisan Da Aka Yi wa Fararen Hula 137


Jakadan Amurka A Jamhuriyar Nijar
Jakadan Amurka A Jamhuriyar Nijar

Gwamnatin Amurka ta yi Allah wadai da harin da aka kai a Nijar, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 137.

Amurka ta ce ta damu matuka game da karuwar hare-hare da tashin hankalin da ake kara samu tsakanin farar hula.

Hari na baya-bayan nan shi ne wanda ya yi sanadin mutuwar fararen hula 137 a yankin Tahoua.

"Muna cike da bakin cikin karuwar hare-hare akan fararen hula, kuma muna kira ga wadanda ke da alhakin daukar kwararan matakai akan masu kai irin wadannan hare-haren, da su dau mataki don ladabtar da su kamar yadda doka ta tanada." Wata sanarwa da kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka, Ned Price ya fitar ta ce.

Price ya kara da cewa Amurka na tare da mutanen Jamhuriyar Nijar, yayin da suka shiga wani zaman makoki na wadanda abin ya shafa.

"Mun dukufa kan yin aiki tare da Gwamnati da jami'an tsaro na Jamhuriyar Nijar, don tunkarar masu tsattsauran ra'ayi da tabbatar da tsaro da ci gaban ga dukkan 'yan kasar Nijar," a cewar Price.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce daga watan Janairu zuwa watan Maris, an kashe fararen hula mama da 290 a hare-hare daban.

Akan dora alhakin hare-haren akan kungiyar ISWAP, Boko Haram da sauran kungiyoyi masu ikrarin jihadi da ke da iyaka da kasar ta Nijar da Mali da Burkina Faso.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG