Buhari: Dole Mu Hada Kai Wajen Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa

Sakataran Gwamnatin Tarayyar Najeriya Mr. Boss Mustapha

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, wadan Sakataren gwamnatin tarayya Mr. Boss Mustapha ya wakilice shi a wannan taro, ya jaddada kiransa na neman hadin kai gabadaya domin yaki da cin hanci da rashawa

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya kalubalanci gwamnonin da ke karkashin jami’iyyar APC da su mara wa gwamnatin tarayya baya wajen yakin da ta ke yi na kauda cin hanci da rashawa.

Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin taron hadin gwiwa tsakanin gwanmonin da ke karkashin APC, da gwamnatin tarayya da aka gudanar a Jos, jihar Filato.

Taron Hadin Guiwa Tsakanin Gwamnonin Dake APC Da Gwamnatin Tarayya A Jihar Filato

Mahalarta taron sun hada da ministoci, da gwamnonin APC, da shugbannin sassan gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki, inda suka tattauna hanyoyin da zasu inganta rayuwar al'umma da suka zabe su, ta hanyar tsaro, kiwon lafiya, Ilmi, da kuma bin gaskiya wajen sarrafa dukiyar al'umma da dai sauran su.

A saurari rahoto cikin sauti daga wakiliyar Muryar Amurka, Zainab Babaji.

Your browser doesn’t support HTML5

Buhari: Dole Mu Hada Kai Domin Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa