Zamu fara Shirin takaitattun labaran wasannin namu ne da gaya muku sunayen yan wasan kwallon kafa na kasar Brazil su guda goma wadanda sune kasar ta bayyanasu a matsayin fitattu a kasar.
Mutun na farko shine Pele, na biyu, Ronaldo, na uku, Garrincha, na hudu, Ronaldinho, na biyar,Romario,na shida,Rivaldo,na bakwai,Zico,na takwas,Socrates, na tara, Jairzinho, sai na goma Kaka.
Sai kuma shahararrun yan wasan kwallon kafa guda goma wadanda suka yi fintinkau ma ‘yan uwansu a iya taka leda, a matakin masu buga wasa a tsakiya, wanda ake kiransu da sunan Midfielders, a fagen wasan kwallon kafa. Mutum na farko shine , Kevin De Brune, dan kasar Begium , dake buga wasa a klu din , Manchester City, Mutum na biyu shine Frankie De Jong, dan Kasar Netherlands yan taka leda a Klub din Barcelona, sai mutum na uku, Pedro González López da ake masa lakani da Pedri, shi dan kasar Sifaniya ne, kuma yana buga kwallo wa Klub din Barcelona, Mutum na hudu kuwa, shine, Jorginho,Yana Klub din Chelsea, shiruwa biyu ne da Italiya dakuma Barazil, Mutum na biyar kuma, shine, Marco Verratti,shi dan kasar Italiyane,yana taka leda a Klub din,PSG, sai mutum a shida, Bruno Fernandes, dan kasar Portugal,yana kwallo a Klub din Manchester United, sai mutum na Bakwai, Paul Labile Pogba, dan kasar Faransa, Mutum na takwas kuwa shine, Kanté N'Golo Kanté, shima dan Kasar Faransa ne, yana wasa a Klub din Chelsea, mutum na Tara shine, Luka Modrić, yana wasa a Klub din Real Madrid, shi dan Kasar Koreshiya ne, mutum na goma, a fagen wasan tsakiya shine, Joshua Walter Kimmich, dan Kasar Jamus,yana Klub din Bayern Munich.
Kasar Qatar mai masaukin baki a gasar kwallon kaf ana duniya da ake Shirin gudanarwa a watanNuwamban wannan shekara ta 2022, ta haramta ayyukan Badala, a lokacin gudanar da gasar, musamman wadanda ba muharram mutum bane, aikata hakan hukuncinsa zaman gidan Yari shekara bakwai.
Har ila yau,masha’a, ta hanyar shaye shaye, da gwan gwajewa, a lokacin da ake fafatawa dakuma bayan an tashi daga wasa, kasar bazata lamunta ba, Kasar Qatar tana gargadin yan kallo,na wasan kwallon duniya na wannan shekara, cewa kasar bata amince,da aikata Badal aba kafin yin aure,kuma babu wani taro don gudanar da Sharholiya.
Hukumar , FIFA, tayi marhabin da wadannan sharudda, sannan ,baki wadanda basa da suna kokuma inkiya guda da juna an hana musu kama daki kokuma zama daki guda. Dabi’ar shaye shaye da sharholiya, a bayantashi daga wasa, zai gamu da mummunan sakamako, inji cewar, Nasser al- Khater, Shugaban hukuar FIFA, na Kasar Qatar, na gasar kwallon Duniya, na shekarar 2022, inda yakara da cewa wannan abu ba al’adarsu bane.
A halin da ake cki kuma , an kera Kwallon da za’a yi amfani dashi a gasar, a kasar Pakistan, don gasar cin kofin kwallon kafa na duniya, Sunan Kwallon dai shine Al Rihla, wato mai tafiya.
Ana saida kwallon kan dalar Amurka $165, a Kasashen Turawan Ingila, ana saida kwallon akan Fam din Ingila £130, ayayinda kasashen dake amfani da kudin Yuro, ansa saida kwallon, €155
Gasar kwallon kafa ta nahiyar Afrika na shekarar 2023 wanda za a gudanar a Kasar Ivory Coast, hukumar Kwallon kafa ta nahiyar Afrika CAF ta dage gasar zuwa shekarar 2024. Shugaban,hukumar kwallon ahiyar Afirka, Patrice Motsepe, ya shaida hakan a taron manema labarai, ranar Lahadi 3 ga watan Yulin wannan sheara a Kasar Morocco. Ya dangantadage gasar, sabili da yanayin Kasar Ivory Coast, a wannan lokaci,bazai kasance mai dadiba, yanzu dai za a gudanar da gasar kwallon Afrikan, tsakanin watan, Janairu da Febrairun shekara ta 2024, idan Allah yakaimu.
Saurari cikakken rahoton Abdulwahab Muhammad:
Your browser doesn’t support HTML5