Shugaban gidan yarin jihar, Jarbas Vasconcelos, ya fada a cikin wata sanarwa cewa ‘yan wata kungiyar fursuna, mai suna Comando Classe A, ne suka saka wuta a dakunan kwanan abokan hamayyarsu na kungiyar Comando Vermelho.
WASHINGTON D.C. —
Akalla fursunoni 57 suka mutu lokacin da aka yi bore a wani gidan yari da ke arewacin kasar Brazil a jiya Litinin.
An dai fara boren ne tun da sanyin safiyar jiya a gidan yarin Altamira da ke arewacin jihar Para.
Shugaban gidan yarin jihar, Jarbas Vasconcelos, ya fada a cikin wata sanarwa cewa, ‘yan wata kungiyar fursunoni, mai suna Comando Classe A, ne suka saka wuta a dakunan kwanan abokan hamayyarsu na kungiyar Comando Vermelho.
An ga hotunan bidiyo da kuma hotuna da wata kafar yada labarai ta nuna yadda wuta take fitowa daga gidan yarin.