Boma-Bomai Sun Fashe a Gombe

Gombe a Bayan Harin Bom, Fabrairu 1, 2015.

Gombe a Bayan Harin Bom, Fabrairu 1, 2015.

Boma-Bomai sun fashe a garin Gombe, na farko ya tashi ne a tsohowar kasuwa ta kofar gabas mace da na miji ne, suka kai harin kunar bakin waken, na biyu kuwa ya faru ne a kusa da Kwata gadin Sojoji da yake kan haryar Dadin kowa.

Wannan tagwayen Boma-Bomai sun yi sanadiyar mutuwar mutane da dama inda wasu kuma da dama suka jirkita, hukumomi da ‘yan agaji ne suka taimaka aka kai wadanda suka ji raunuka asibiti.

Wannan shine karo na uku, da ‘yan kungiyar Boko Haram, ke kari hari kusa da Quarter guard din Sojoji da yake kan hanyar zuwa Dadin kowa.