Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nan da Wata Daya 'Yan Gudun Hijira daga Najeriya a Chadi Zasu Fi Dubu Talatin


Wasu 'yan gudun hijira.
Wasu 'yan gudun hijira.

Majalisar Dinkin Duniya ta tsugunar da 'yan gudun hijira daga Najeriya a cikin kasar Chadi.

Cibiyar tsugunar da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta fada jiya Laraba cewa, tashin hankali da ta’addanci ya tilasa wa‘yan Najeriya dubu goma sha hudu kaura domin tsira da rayukansu zuwa kasar Chadi a cikin watan nan na Janairu.

Mayakan Kungiyar Boko Haram masu tsats-tsauran ra’ayin addinin Islama a arewacin Najeriya ta kwace wani sansanin soja ta kuma kai hari Baga dake kusa da tekun Chadi farkon wannan watan.

Wadansu sun ce dubban mutane ne suka rasu.

Da dama cikin ‘yan Najeriyan dake gudun hijira sun gayawa jami’an Majalisar Dinkin Duniya labarai masu sosa rai kan harin kungiyar Boko Haram, suka ce mayakan kungiyar sun rika harbin mutane dake kokarin tserewa cikin kwale-kwale.

Wani mutum yace ya ga gawarwakin mata da kananan yara suna kan ruwan tafkin.

Kwanan nan Majalisar Dinkin Duniya ta gina sansanin ‘yan gudun hijira a Dar es Salam babban birnin kasar Chadi. Cibiyar tsugunar da ‘yan gudun hijiran tana kiyasin cewa kimanin ‘yan gudun hijira dubu talatin ne zasu isa Chadi kafin karshen shekara.

‘Yan ta’addan Boko Haram dake neman kafa shari’ar Islama a Najeriya, sun kashe dubban mutane daga shekara ta dubu biyu da tara.

XS
SM
MD
LG