Yawan mutane da suka mutu a sakamakon hare haren da aka kai ofisoshin jaridar This Day a Abuja da Kaduna ranar Alhamis ya karu zuwa mutane tara.
'Yan jarida a Nigeria sunce ba zasu daina baiyanawa jama'a abubuwan da suke faruwa ba. Sunyi wannan furucin ne bayan hare haren da aka kai ofisoshin jaridar This day a Abuja da Kaduna.
Dama anyi tsamanin cewa kungiyar Boko Haram ce ta kai hare haren, domin a baya ta yiwa kafofin yada labaru barazana. Sai kuwa gashi wata jaridar yanar gizo, The Premiun Times ta buga labari a ranar Alhamis da dare cewa kungiyar Boko Haram tayi ikirarin cewa ita keda alhakin kai hare haren..
Ita wannan jaridar tasa hiarar data ce tayi da mai magana da yawun kungiyar Boko Haram a ranar Alhamis da dare. Shi mai magana da yawun kungiyar da ake cewa Abu Qaqa yace hare haren maida martani ne ga kafofin yada labarai domin suna yada labarun da suka ce na nuna son kai ne dangane da aiyukan kungiyar. Yace kungiyar Boko Haram ta auna ofisoshin jaridar This Day, domin tafi sauran kafofin yada labaru laifi,
Har yanzu dai ba'a tantance sahihanci wannan hirar da aka ce anyi da Abu Qaqa mai maigana da yawun kungiyar Boko Haram, daga wata kafa ta fisabillahi ba.