A garin Mongumeri, ‘yan ta’addan masu yawan gaske sun kai hari kan tawagar ‘yan sanda ta musamman a ranar Laraba a wani artabu na tsawon sa’a guda, kamar yadda majiyar ‘yan sanda ta shaida wa Muryar Amurka.
Kwamishinan ‘yan sanda jihar Borno, CP Abdu Umar ya tabbatar da faruwar harin. Ya shaida wa manema labarai cewa an kashe dan sanda a musayar wuta da ‘yan ta’addan. Ya kuma ce, motar ‘yan sandan da ‘yan ta’addan suka yi awon gaba da ita a yayin harin, an samu nasarar kwato motar da taimakon sojojin da ke yankin.
“Boko Haram sun je Mongumeri suka kai hari a inda muke, wato tawagar mu ta ‘CRACK Team’. Sun zo da yawa, suna harbin bindigogi. Mun yi musayar wuta da su. Mun rasa daya daga cikin mutanenmu amma mun dakile harin. Sun tafi da daya daga cikin motocinmu amma daga baya sojoji sun kwato ta,” inji CP Umar.
Ya ce an dauke gawar dan sandan da aka kashe daga inda aka kai harin.
Ya ce lamarin ya faru ne a karamar hukumar Dikwa a ranar Laraba yayin da Boko Haram suka yi wa wasu masunta kwanton bauna tare da kashe 25 daga cikinsu.
"Daya ya samu rauni kuma yana samun jinya," in ji CP Umar.
Wasu mazauna yankin sun ce wadanda harin ya rutsa da su suna diban tarkace da karafa ne a kauyukan da aka lalatar da hare-haren ta’addanci na tsawon shekaru, a lokacin da ‘yan Boko Haram suka yi musu kwanton bauna.
Abubuwan da suka faru sune manyan hare-hare na farko a Borno a bana. Yankin ya sami kwanciyar hankali na dan lokaci.
Ga dai sautin rahoton Haruna Dauda Biu:
Your browser doesn’t support HTML5