Mayakan Boko Haram da ISIS sun tsara kai hare-haren ta’addancin ne a wasu yankunan jihar Adamawa da dajin sambisa gabani da kuma lokutan bukukuwan Kirsimeti, kafin sojojin Najeriya su gano shirin su kuma dauki mataki.
Jami'in sadarwa na aikace-aikacen rundunar sojojin Najeriya, kanar Aminu Ilyasu, ya bayyana cikin wata sanarwa da ya sanyawa hanu cewa, wani shirin gama aiki na kai farmaki na musamman mai take Operation Rufe Kofa dake karkashin Rundunar Operation Lafiya Dole ne ya cimma dakile kai hare-haren na ta’addanci.
Kanar Ilyasu, ya ce dakarun Bataliya ta 192 sunyi wani aikin sintiri a wasu yankuna biyar dake karamar hukumar madagali, inda suka gano tare da kai mummunan farmaki ga yan ta'addar, wanda ya yi masu kaca-kaca, baya ga kone gonarsu da kuma ma'adanar boye abincinsu dake cikin karkashin kasa.
Tuni dai babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Najeriya, Janar Tukur Yusufu Buratai, ya jinjinawa dakarun bisa wannan namijin kokari sannan ya kara zaburar dasu da su gaggauta kawo karshen burbushin mayakan na Boko Haram.
Ga karin bayani a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5