BOKO HARAM: Sojojin Najeriya Na Anfani da Sabon Salon Yaki

Hafsan Sojojin Najeriya Janar Tukur Yusuf Buratai

Rundunar Sojin Najeriya tayi bayani kan irin sabon salon da take dauka na yaki da kungiyar Boko Haram a shiyar arewa maso gabas.

Sabon salon shi ne sanadiyar nasarar da rundunar take samu a yakinta da 'yan ta'adan.

Mukaddashin kakakin rundunar Kanal Sani Usman Kukasheka yayi bayanin abubuwan da suka basu nasara. Sun samu karin sojoji da kayan aiki da karin makamai.

Bugu da kari rundunar ta samu wani sabon hadin kai da jami'an tsaro da daukacin mutanen Najeriya gaba daya da kasashen dake makwaftaka da Najeriya..

To saidai duk da nasarorin da rundunar ke samu mutane dake zaune a wasu kauyukan jihohin Borno da Yobe suna cigaba da samun hare-hare daga 'yan kungiyar Boko Haram din.

A kan wadan nan hare-haren Kanal Kukasheka yace abun takaici ne amma saboda mayakan sama na kaiwa 'yan ta'adan hari basu da wurin gudu. Daidai na sulalewa su shiga kauyuka inda suke satar abinci da ruwa bayan sun yi kashe kashe kafin su koma inda suka fito. Yace amma basu yi kasa da gwiwa ba. Duk inda suka ji irin wannan labarin suna kai dauki.

Saidai ya yi gargadin cewa sojojin Najeriya ba zasu iya kasancewa koina ba a kowane lokaci amma suna bakin kokarinsu idan kuma aka sanar dasu zasu kai dauki.

Dangane da wadanda aka yiwa hukunci lokacin gwamnatin da ta shude Kanal Kusheka yace sojoji 5332 ne abun ya shafa. Yace an wankesu an kuma mayar dasu aiki. Yanzu suna samun horaswa ta musamman. Akwai wasu hukunce-hukunce da ba'a ambata ba. Akwai kuma wasu sharudodi da har yanzu ana cigaba dasu saboda abun ya shafa sun daukaka kara. Irinsu basa cikin wadanda aka warware matsalarsu.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina.

Your browser doesn’t support HTML5

BOKO HARAM: Sojojin Najeriya Na Anfani da Sabon Salon Yaki