Jami'an tsaron Najeriya sun dade suna yaki da ta'adanci a kasar amma kuma sun yi kamarin suna wajen tattara mutane su tsaresu na shekara da shekaru ba tare da gurfanar dasu gaban shari'a ba.
Yayinda yake fafutikar neman zabe shugaba Buhari ya yi alkawarin kiyaye dokokin kasar tare da baiwa jama'a hakinsu duk da cewa zai yaki Boko Haram da kowane irin ta'adanci babu sani babu sabo.
A Najeriya kundun tsarin mulkin kasar ya bayyana hakin da ya rataya akan hukumomin tsaro dangane da duk wanda suka kama da zargin aikata wani laifi.
Barrister Yakubu Saleh Bawa masani akan harkokin shari'a yace kundun tsarin mulkin kasar ya bayyana cewa duk laifin da mutum ya aikata ko wanda bai cancanta a bashi beli ba to kada a tsare mutum fiye da wata daya kafin a gabatar dashi gaban shari'a.
Wanda aka ba beli to dole ne a gabatar dashi gaban shari'a cikin watanni uku.To amma a Najeriya sai a ajiye wanda ake zargi da aikata laifi shekara daya har biyar ko bakwai ba'a gurfanar dashi gaban shari'a ba. Jami'an tsaro sai su ce wai suna bincike.
Amma kundun tsarin mulki yace tsare mutum fiye da lokacin da tsarin ya kayyade cin zarafin wanda aka tsare ne. Ko da ma dan Boko Haram ne babu dokar da ta yadda a tsareshi fiye da wata daya ba'a gurfanar dashi gaban kuliya ba.
Kasar Chadi ta gurfanar da 'yan ta'ada nan da nan ta kuma yanke masu hukunci ba tare da bata lokaci ba duk da cewa kasa ce karama idan aka kwatanta da Najeriya. Jama'a sun yi na'am da hukuncin.
Barrister Yakubu Saleh Bawa ya koka da yadda har yanzu hukumomin tsaron kasar na cigaba da tsare daruruwan mutane da ake zarginsu da kasancewa 'yan Boko Haram ba tare da gurfanar dasu gaban kuliya ba.
Galibin samamen da jami'an tsro ke kaiwa irin na kan mai uwa da wabi ne. Shin ina matsayin wadanda aka kama?
Manjo Janar Adamu Baba Abubakar daraktan sashen mulki na hekwatar sojojin kasa yace sun kafa kwamitocin hadin gwiwa biyu da zasu yi bincike su tantace 'yan ta'ada daga mutanen da ake tsare dasu. Cikin mutane 504 an samu hujjojin gabatar da 350 gaban kotu har ma an tura batunsu ga ma'aikatar shari'a ta tarayya.
To saidai wasu masana tsaro da yaki da ta'adanci irinsu Dr. Muhammad Aliyu Dengel na jami'ar Maiduguri na ganin ya kamata gwamnati ta kirkiro kotuna na musamman domin yiwa 'yan ta'ada shari'a. Wadan nan kotunan zasu yi maganin bata lokaci da yanzu ake fuskanta. Yakamata a yi masu hukunci da wuri idan kuma ba haka ba za'a shiga damuwa da cigaba da sabawa doka da karya hakin wadanda ake tsare dasu.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina.