Rundunar tace ta samu nasarar fatattakar wasu 'yan kungiyar Boko Haram a dajin Sabisa tare da cafke wasu gaggan kungiyar biyu.
Kanar Sani Usman Kukasheka mataimakin daraktan hulda da jama'a na rundunar sojoji shi ya rabtaba hannu akan sanarwar da aka rabawa manema labarai.
Sakamakon aman wuta da sojojin sama keyi ya sa 'yan kungiyar suka yi kokarin tserewa amma aka kamasu. Sojojin sun kuma hallaka wasu da dama. Sun gano makamai masu dimbin yawa tare da lalata wasu.
Sanarwar ta kara da cewa sojoji sun kwace wasu motoci guda bakwai da babura da harsashai da albarusai da maharan ke anfani dasu. Sanarwar ta kara da cewa har yanzu sojoji na cigaba da farautar wadanda suka arce.
Kanar Sani Usman ya yi karin bayani wa Muryar Amurka. Yace wasu 'yan ta'adan ne suka danno da motoci suna gudun lugudan wutar da mayakan sama ke jefa masu sai suka far masu.
'Yan ta'adan sun so su gudu zuwa wajen Gwozah kafin sojoji su yi artabu dasu. Na aka lalata motocinsu da makamansu kana aka kashe ko cafke wasusnsu.
Ga rahoton karin bayani daga rahoton Haruna Dauda Biyu.
Your browser doesn’t support HTML5