Boko Haram: Shugaban Nijar Ya Kai Ziyara Yankin Diffa

Shugaban kasar Nijar Issouhou Mahamadou ya kai ziyara yankin Diffa dake kudu maso gabashin kasar da nufin karfafawa jami’an tsaro gwiwa a yakin da suke kafsawa da Boko Haram.

Shugaba Issouhou ya kai ziyarar kwana guda birnin Diffa ranar asabar 9 ga watan Nuwamba yankin dake makwaftaka da kasashen Chadi da Najeriya, Yankin da ya shafe shekaru hudu yana fama da hare haren mayakan kungiyar Boko Haram.

Rangadin dai ya fara ne daga barikin sojoji ta Zone de Defense No 5, inda shugaban ya jinjinawa dakarun kasar, saboda yadda suka jajirce wajen tabbatar da tsaro.

Ya ce ina yabawa yadda kuke gudanar da aikin kare al’umma da kuyoyi cikin hikima da kwarewa tare da mutunta hakkokin dan Adam. Mun yi asarar mazaje a fagen fama, amma kuma abokan gaba sun ji a jikinsu sosai a tsawon shekarun da kwashe, domin alkalumma sun yi nunin mun hallakawa Boko Haram mutane 1400 a tsawon wannan lokaci, koda yake yawansu zai iya zarta haka kasancewar ba kasafai ‘yan ta’adda ke barin gawarwakinsu a fagen yaki ba.

Shugaban ya ci gaba da cewa ku sani duk wanda yake da al’uma tare da shi ya gama cin yaki, saboda haka nake baku umarnin ku mayar da hankali wajen samar da bayanan sirri ku karfafa matakan sintiri da na kai hare hare ba kakautawa.

Ya ci gaba da cewa, na yi Imani ta’addanci komai dadewa ta’addanci zai zo karshe domin manufar da mau wannan akida ke karewa ba ta da nasaba da addinin musulunci.

Da yake ci gaba da wannan ziyara shugaban ya isa kauyen Gueskerou domin jajantawa talakawa game da asarar da ambaliyar ruwan Komadougou ta haddasawa gonakin shinkafa da tattasai yayin da aiyukan kiwo da kamun kifi suka tsaya cik. Ministan cikin gida Bazoum Mohamed na cikin tawagar ta Issouhou Mahamadou.

Magajin garin Diffa Malan Brah Mamadou dake magana da yawun al’ummar wannan yanki ya yaba da wannan ziyara da ya ce za ta karawa talakawa kwarin gwiwa.

Ga karin bayani a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Boko Haram: Shugaban Nijar Ya Kai Ziyara Yankin Diffa