Wadanda suka halaka sun hada da mata da kananan yara yayinda wasu da dama kuma suka jikata..
Tsohon shugaban karamar hukumar Mr Maina Ularamu yace mata biyu ne suka kai harin. Sun shiga jama'a suna cewa wani abu ya faru dasu. Da mutane suka taru domin su taimakesu sai suka tayar da bamabaman dake jikinsu.
Banda matan mazajensu dauke da bindigogi sun boye. Da mutane suka fara gudu sai wadanda suka boye suka fara harbinsu.Sun kashe mutane kana sun kone gidaje.
Hukumomin tsaro a jihar sun tabbatar da aukuwar lamarin. Kakakin rundunar 'yansadan jihar DSP Usman Abubakar yace sun kashe mutane 11 kuma su 'yan kunar bakin waken 'yan mata ne.
Ko ranar Asabar ma sai da 'yan Boko Haram suka yiwa sojoji kwantan bauna a yankin yayinda suka batar da kama ta sa kayan 'yan banga. Sun tare hanya suna barna.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5