Da yake magana a wani taro kan batun tsaro jiyaTalata a birnin Paris, Farhat yace kimanin 'yan kasar Tunisia dubu sun shiga kungioyi daban daban dake ikirarin suna jihadi, kuma da irin koma bayan da kungiyar ISIS take samu a baya bayan nan, suna iya komawa kasar, kuma babu wani shiri na tunkarar irinsu a arewacin Afirka.
Rahotanni da kafofin yada labarai ciki harda da AFP, da Reuters, sun ce duk da hasarar yankuna da suke karkashinta, kungiyar ISIS tana ci gaba da samun sabbin magoya baya, da samun makamai, kuma tana ci gaba da kaddamar da hare haren ta'adanci a fadin duniya.
A wani sharhi da ya gudanar, kamfanin dillancin labarai na Reuters, yace kungiyar ISIS tana kaddamar da sabbin hare haren ta'addanci cikin kasa na kwanaki hudu kowane mako daga watan Yunin bana zuwa yanzu.