Sunyi ganawa ta gaba da gaba ne kan yadda kasar Kamaru take fama da hare haren kungiyar Boko Haram dama tada bama bamai na kunar bakin wake da kungiyar Boko Haram ke yi a arewacin kasar Jamhuriyar Kamaru.
A halin yanzu dai kasar Kamaru ta karbi ‘yan gudun hijira dama da dubu dari da hamsin wadanda suke gujewa hare haren kingiyar Boko Haram, wadanda suke makwabtaka daga kasashen dake makwabtaka da Kamaru, galibi daga arewa maso gabashin Najeriya.
Banda haka kuma, kasar Kamaru na fama da kwararar ‘yan gudun hijira daga kasar Afrika ta tsakiya yankin Bangi kuma ‘yan tawayen Bangi.
Yanzu haka dai akwai kimanin ‘yan gudun hijira dubu dari biyar da suka hada da ‘yan kasar Kamaru da suka rasa matsugunansu sakamakon wadannan tashe tashen hankalin.
Ga rahoton da wakilin Sashen Hausa da Mamahad Awal Garba ya aiki daga birnin Yaounde, kasar Kamaru.
Your browser doesn’t support HTML5