Gwamnatin kasar Kamaru ta yanke shawarar cewa dakarun tsaron da kasar Amurka ta turo kasar ta Kamaru zasu kafa sansanin su ne a Garwa dake jahar arewa.
Sojojin na Amurka zasu yi Shawagi akan iyakokin kasar Kamaru Najeriya, Chadi da jamhuriyar Nijar, domin kai hare hare ga ‘yan Boko Haram, da kuma gano maboyar su dake tafkin Chadi, inda ‘yan kungiyar Boko Haram ke aikata aika aika, da kuma gano wasu bayanai na siri.
Wani tsoho Jandarma mai suna Ali Haya, ya ce kasancewar Sojojin Amurka, shahararru ne a duniya taimakon da suka kawo ma kasar Kamaru yana da tasiri sosai.
Shi kuwa Ahmadu Muhammadu wani dan kasuwa tsakanin Najeriya da Kamaru cewa yayi tamakon da Amurka, ta kawo zai kara karfafa wa jama’ar yankin karfin gwiwa.
Wani dan rajin kare hakkin bil Adam, Malam Rabiu Ismaila, ya ce ana tsamanin kasar Faransa ne zata fara kawo taimakon amma sai gashi Amurka wandada suke gwanaye wajen yaki da ta’addanci su ne suka kawo taimako.