‘Dururruwan ‘yan mata da mata da yara ‘kanana na cigaba da karbar taimakon agajin gaggawa a wani sansani, bayan da aka ceto su daga dajin Sambisa dake arewa maso gabashin Najeriya, mayakan kungiyar Boko Haram ne dai suka tsaresu na tsawon lokutan da ba’a tabbatar ba.
Hukumar agajin gaggawa ta Najeriya tace an dauki matan da yara su 275 zuwa sansanin Malkoho dake yankin Yola, domin a basu kulawar kiwon lafiya da abinci da kuma shawarwari bisa la’akari da irin ukubar da aka gasa masu.
Wani jami’in sansanin yace yawancin yaran ana basu kulawa kan ramewa da rashin samun abinci mai gina jiki. Su 21 daga cikin su kuma ana basu kulawa domin ciwon da suka ji a dalilin harbinsu da akayi. Mafi yawancin matan da kungiyar Boko Haram ta kama suna amfani dasu ne wajen bauta da kuma kariya.
Jami’ai dai sunce suna kokarin su ganoinda matan da yaran suka fito, domin babu alamun sun fito ne daga inda aka ajiye ‘yan matan nan sama da ‘dari biyu da aka sace a garin Chibok a shekarar data wuce.