Boko Haram: An Kama Tsohuwar Matar Mamman Nur

Jami'an Bada Kariya Ga Fararen Hula Na Civil Defense

Rundunar bada kariya ga fararen hula da ake kira Civil Defense, ta gurfanar da wasu mata biyu ga manema labarai wadanda ake zarga da kokarin shirya kai hari a wasu guraren dake cikin garin Maiduguri.

‘Daya daga cikin ‘yan matan mai shekaru 15 da haihuwa Fatima Kabir, ta ce ta kwashe shekaru biyu a dajin Sambisa, ta yi aure har sau uku mijin ta na farko shine Mamman Nur ‘daya daga cikin kwamandojin Boko Haram, haka kuma yanzu haka tana ‘dauke da juna biyu, kuma gwaje gwaje sun nuna cewa tana ‘dauke da kwayar cutar HIV.

Ita ma Amina Salisu, mai shekaru 14 da haihuwa ta ce ita ‘yar asalin garin Gulok ce lokacin da ‘yan Boko Haram suka shiga garin suka kwashe su baki ‘daya tare da iyayenta.

Haka kuma Amina Salisu ta tabbatar da cewa ita ma ta yi aure a dajin Sambisa har sau biyu.

Kwamandan rundunar Civil Defense Ibrahim Abdu, shine ya gurfanar da matan wanda yace an kama su ne lokacin da aka shigo da su garin Maiduguri, don kokarin duba inda zasu kai hari.

An kuma nunawa manema labarai wasu jarkokin Man Fetur da aka ce wasu ne suka gudu su barsu a baya, wanda ake zargin ana shirin fita da Man ne zuwa wasu wurare don aikata abin da bai kamata ba.

Domin karin bayani saurari rahotan Haruna Dauda.

Your browser doesn’t support HTML5

Boko Haram: An Kama Tsohuwar Matar Mamman Nur - 4'39"