Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za a Iya Kwashe Shekaru Kafin Kubutar Da ‘Yan Matan Chibok – in ji ‘Dan Ali


ABUJA: Shugabannin Addini Sun Yi Maci Akan 'Yan Matan Chibok
ABUJA: Shugabannin Addini Sun Yi Maci Akan 'Yan Matan Chibok

Ministan tsaron Najeriya ya ba da kashedin cewar mai yiwu wa a kwashe wasu shekaru kafin a kubutar da ‘yan matan Chibok da yan ta’addan Boko Haram suka yi garkuwa da su.

Da yake zantawa da sashen Hausa na Muryar Amurka, Janar Manir Dan Ali mai ritaya, ya ce sojojin suna kutsawa a inda mayakan Boko Haram suka boye a cikin dajin Sambisa wanda girmansa ya mamaye wasu sassan jihohi uku a Arewa maso gabashin Nigeria.


Ya ce ya dauki lokaci mai tsawon gaske kafin Amurka ta gano Osama Bin Laden wanda ya shirya harin ranar tara ga watan Satumbar shekarar 2001.

Ya ce Amurka ta kwashe shekaru takwas zuwa goma kafin ta gano Bin Laden.

A cewar Dan Ali suna ci gaba da yakin da suke yi a dajin Sambisa a kowane lungu na cikin dajin.

Janar Dan Ali, ya zanta da Muryar Amurka a daidai lokacin da masu fafutukar ganin an kwato 'yan matan suke bukin cika shekaru uku da yin garkuwa da 'yan matan.

Kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da dalibai mata 276 na makarantar sakandaren garin Chibok dake Arewa maso gabashin kasar a ranar 14 ga watan Afirilun 2014.

Ya zuwa yanzu ba a gano 195 a cikin 'yan matan ba.

Duk da irin nasarori da aka samu a yaki da Boko Haram, gazawar gwamnatin wurin kwato ko gano inda 'yan matan suke, ya dusashe nasarorin da sojojin suke samu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG