Jakadan Amurka Mr. James Enwistle ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da wakilin Muryar Amurka Sanusi Adamu da ke Yola, babban birnin jahar Adamawa, a lokacin da ya kai ziyara sansanin ‘yan gudun hijra.
Sansanin ‘yan gudun hijran na Yola yana dauke ne da ‘yan mata da mata da sojojin Najeriya suka kubutar daga dajin Sambisa a 'yan kwanakin da suka gabata.
“Ban taba fuskantar wani bala’i ba, ban kuma san yanayin da zai sa na fita daga cikin hayyaci na ba, amma da na ga wadannan mata da yara, sai na rasa ta inda zan fara tunanin irin wahalhalun da suka fuskanta musamman ganin cewa nima ina da yara biyu.” In ji Mr. Enwistle.
Ya kuma kara da cewa “a matsayi na jakada da dan adam, dole ne mu nemi hanyar da za mu taimaka.” Mr Enwistle y ace.
Jakadan na Amurka ya ce ya kai ziyarar ne domin ya ganewa idonsa irin halin da ‘yan gudun hijran ke ciki tun bayan da aka ceto su.
Mr. Enwistle ya kara da cewa Amurka na taimakawa da shawarwari wajen yaki da ta’ddanci a Najeriya yana mai cewa za su kara taimakwa kasar musamman ma al’umar da ke arewa maso gabashin.
Ga karin bayani a rahoton Sansui Adamu:
Your browser doesn’t support HTML5