Biyu Daga Cikin Iyayen Daliban Islamiyyar Tegina Da 'Yan bindiga Suka Yi Garkuwa Da su Sun Mutu

Dalibai 'yan makaranta.

Hukumar Makarantar Islamiyyar Salihu Tanko, dake garin Teginan Jihar Nejan Najeriya da 'yan bindiga suka yi garkuwa da dalibanta a ranar Lahadin da ta gabata, ta tabbatar da mutuwar 2 daga cikin iyayen daliban sakamakon tashin hankalin sace masu 'ya'ya.

Shugaban Makarantar, Abubakar Garba Alhassan, ya shaida wa Muryar Amurka cewa fargaba da tashin hankali ne ya sa wadannan iyaye suka yanke jiki suka fadi a karshe kuma rai ya yi halinsa.

Gwamnatin jihar Nejan ta bakin mataimakin gwamnan Alh. Ahmed Muhammad Ketso, ta kira wani taron manema labarai inda ta bayar da tabbacin cewa tana iya kokarinta wajen kubutar da wadannan dalibai.

A halin da ake ciki dai Hukumar Makarantar ta ce yara 145 aka tabbatar suna hannun 'yan bidigar a halin yanzu, sabanin labarin dake nuna sama da 200 ne.

A wani labarin kuma gwamnatin jihar Nejan ta sanar da hana sana'ar kabu-kabu ko achaba a cikin birnin Minna fadar gwamnatin jihar saboda dalilai na tsaro.

Karin bayani akan: jihar Nejan, Abubakar Garba Alhassan, Muryar Amurka, Nigeria, da Najeriya.

Matsalar satar dalibai a arewacin Najeriya ta zama ruwan dare, inda a lokuta da dama akan yi garkuwa da su don neman kudin fansa.

A tsakiyar watan Fabrairu, ‘yan bindigar suka sace dalibai 27 makarantar kwana da ke Kagara a jihar ta Neja, wacce ke tsakiyar arewacin Najeriya

An sako daliban bayan da suka kwashe wani tsawon lokaci a hannun 'yan bindigar.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Biyu Daga Cikin Iyayen Daliban Islamiyyar Tegina Da 'Yan bindiga Suka Yi Garkuwa Da su Sun Mutu