Biyan Tsoffin Masu Mulki Fansho Barnar Kudi Ne - Lauya

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Abdul'aziz Yari

Batun kudin fansho da alawus-alawus da tsofaffin gwamnonin jihohin Najeriya ke karba a kowane wata, ba wani sabon labari bane.

A cewar wani lauya mai zaman kansa a Jos da ke jihar Filato, Lawal Ishaq, dimokradiyyar Najeriya ita ce take cinye kudin kasar, shi ya sa ba'a iya yi wa talaka aiki.

A cewar shi, da yawan 'yan Najeriya, ba su da masaniyar makudan kudaden da tsofaffin masu rike da ragamar mulkin jihohin ke karba.

Barista Yakubu Sale Bawa, Shugaban Kungiyar lauyoyin jihar Pilato, ya ce almubazzaranci ne a rika ba tsofaffin gwamnonin irin wadannan makudan kudade.

Batun biyan tsoffin gwamnoni kudaden fanshosu, ya taso ne, bayan da tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari, ya yi korafin ba a biyan shi kudaden fanshonsa, lamarin da ya sa gwamna mai ci, Bello Matawalle ya soke dokar da ta ba da wannan dama.

Lamarin ya janyo ce-ce-ku-ce, ya kuma haifar da muhawara a tsakanin 'yan Najeriya kan yadda ake biyan kudaden fansho ga tsoffin jami'an gwamnati.

Saurari cikakken rahoto cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Biyan Tsoffin Masu Mulki Fansho Barnar Kudi Ne - Lauya