Bayan gabatar da wani kuduri da 'yan majalisar dokokin jihar Zamfara suka yi na soke dokar ba tsofaffin gwamnoni da mataimakan su, wasu makudan kudade bayan wa'adin mulkin su, a safiyar yau gwamnan jihar Zamfara Alhaji Bello Muhammad Matawalle, ya rattaba hannu akan wannan kudurin. Abinda ke nufin yanzu babu wani tsohon gwamna ko mataimakin gwamna da zai sake karbar wasu kudade daga ranar da suka kammala wa'adin mulkin su a jihar.
Wannan matakin na zaman maida martani akan wata wasika da tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdul'aziz Yari ya rubutawa gwamnan Zamfara a kwanan nan, yana neman a ba shi kudadden da dokokin jihar suka amince a ba duk wani zababben gwamna har bayan ransa.
Matawalle ya ce ba shi da niyyar karbar kudi daga gwamnati na fansho nan gaba, domin bai ga dalilin karbar kudaden da ya kamata a yiwa jama'a aiki dasu ba don samun ci gaba.
Jihar Zamfara, dake arewa maso yammacin Najeriya na fuskantar matsaloli da yawa musamman ta fannin tsaro, wannan na daga cikin dalilan da suka sa gwamnan ya yanke wannan hukuncin. Gwamnan ya ce bai dace a ce shugabanni su karbi wadannan makudan kudaden ba, domin talakawa ya kamata a taimakawa kamar ta bangaren ilimi, kiwon lafiya, da sauran su.
Gwamna Matawalle kuma yi bayani game da batun kama duk wanda zai shigo jihar ya haddasa tashin hankali, ciki har da shugabanni ko tsofaffin shugabanni, yana mai cewa duk wanda ya taka doka zai fuskanci hukunci.
Ga tattaunawar cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5