Waiwaye Kan Wasu Muhimman Al'amura Da Suka Faru A 2023

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya yi da karbar mulki daga hannun shugaba Muhammadu Buhari, a yayin bikin rantsu a Abuja, Monday, May 29, 2023.

Shekarar miladiyya wato da ta fara lissafi daga haihuwar Annabi Isa alaihissalam ta 2023 ta zo karshe a Lahadin nan.

Shekarar na daga cikin shekarun da za’a rinka tunawa a tarihin Najeriya da ma duniya baki daya.

Misali, a shekarar ce aka gudanar da babban zabe a Najeriya, inda a karo na farko tun 2003 tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ba ya cikin takarar saboda ya kammala wa'adin mulkinsa na tsawon shekaru 8.

Shan rantsuwar sabon shugaba Bola Tinubu da ya lashe zabe a inuwar jam’iyyar APC da ta sake zarcewa kan mulki na daga cikin manyan al'amuran da suka faru a 2023..

Obi Da Tinubu Da Atiku

Dan takarar PDP Atiku Abubakar da na Leba Peter Obi sun yi watsi da sakamkon zaben.

A wannan shekarar ne dai fitaccen malamin addinin Islama Sheikh Abubakar Giro Argungu ya rasu yayin da a bangaren siyasa kuma Allah ya karbi rayuwar tsohon kakakin majalisar wakilai Ghali Umar Na'abba.

Ghali Na'abba

A Jamhuriyar Nijar kuma sojoji karkashin Janar Abdulrahmane Tchiani sun kifar da gwamnatin farar hula ta Mohamed Bazoum, inda hakan ya kawo daukar matakin kungiyar raya tattalin arziki kasashen Afirka ta yamma, ECOWAS na rufe kan iyaka.

Janar Abdouramane Tchiani

Lauyoyi daga Nijar da suka hada da Metri Isma’il Tambo Mousa, sun shigar da kara kotun ECOWAS don neman a janye takunkumin. Kotun dai ta yanke hukuncin korar bukatar.

Baya ga ballewar rikici a Sudan tsakanin shugaban sojan kasar Abdelfatah Burhan da na ‘yan sa-kai Mohammed Hamdan Dagalo, gagarumin yaki ya barke tsakanin Isra'ila da 'yan Hamas, inda bayan harin 7 ga watan Oktoba da Hamas ta kai ketaren shingen Isra’ila, martanin Isra’ila ya yi sanadiyyar dubban rayuka.

FILES-SUDAN-CONFLICT-ARMY-POLITICS-BURHAN

Jakadan Falasdinu a Najeriya, Abdallah Shawesh, ya bukaci shigar da kayan agaji yankin Gaza.

A can Rasha kuma da ke ci gaba da yakin mamaye Ukraine da kasashe yamma ke dauka a matsayin keta haddin kasa mai ‘yanci, jirgi ya fadi cikin yanayi na mamaki da ya hallaka shugaban rundunar haya ta Wagner, Yevgeny Prigozhin da ya yi takun-saka da shugaban Rasha Vladimir Putin.

Shugaban Rasha Vladimir Putin

Shekarar na karewa da batun tsadar dala a Najeriya da ta sa ajiye mafi yawan kudi don kujerar hajji Naira miliyan 4.5, inda shugaban hukumar alhazan Jalal Arabi ke cewa ana daukar duk matakan samun maslaha.

Hakika ko a sauyin yanayi na sanyi da zafi ko hamada a kudancin Sahel na nunawa duniya muhimmancin sauya dabarar rayuwar yau da kullum.

Saurari cikaken rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya:

Your browser doesn’t support HTML5

Waiwaye Kan Wasu Muhimman Al'amura Da Suka Faru A 2023.mp3