Ministan kudin Britaniya Philip Hammond, yace kasar sa zata ci gaba da cika alkawuran da ta yiwa kungiyar tarayyar turai a yayin da zata ci gaba da karfafa dangantakar harkokin kasuwanci da sauran kasashen duniya.
WASHINGTON, DC —
Philip Hammond ya fadawa yan jarida a yau Juma’a a Brussels, inda Ministocin kudi na tarayyar turai suka taru domin halartar taron da suka saba yi akan harkokin tattalin arziki da kuma harkokin kudi wato (ECOFIN) a takaice.
Ministan yace “Har yanzu Birtaniya cikakkiyar yar kungiyar tarayyar Turai ce, sannan nazo nan yau domin tattaunawa da takwarorin aiki na da ministocin kudi.” Hammond ya kara da cewa “zamu ci gaba da daukar dawainiyar babban gurbi. Zamu ci gaba da mutunta dokoki da ka’idodin kungiyar tarayyar Turai har tsahon lokacin da muke cikin kungiyar”.