Birtaniya Ta Zabi Ficewa daga Kungiyar Tarayyar Turai

'Yan Birtaniya da suka goyi bayan kasar ta ciga da kasancewa cikin tarayyar Turai suna mamakin sakamakon zaben

Yayin da ake daf da kammala kidayar kuriar da aka jefa na ko Birtaniya taci gaba da zama cikin kungiyar tarayyar Turai ko a’a masu neman a fice ne ke kan gaba a wannan kuriaar mai cike da tarihi

Daga yanzu dai ana iya bayyana sakamakon wannan kuriaar da aka jefa

Mutane sun fito da dama wajen jefa wannan kuriaar domin ko yana da nasaba da harkokin shige da fice da diyaucin kasa,tsaro da kuma makomar tattalin arzikin kasar ta Birtaniya

Jagorar kanfen na a fice daga kungityar Nigel Farage tuni yake bayyana cewa sune keda nasara .

Nigel Farage, madugun masu son Birtaniya ta fice daga tarayyar Turai

Rashin sanin tabbas game da wannan kuriaar har yasa kudin kasar na Birtaniya wato Fam ya fara saukowa da wurin kashi biyar a daren jiya a landan

An rufe runfunar jefa kuria kamar yadda aka shata za a yi, duk ko da ruwan saman da akayi kamar da bakin kwarya wanda ya haifar da ambaliya a kundacin Engila, kuma ya haifar da cunkoson motoci da ya tilasta rufe wasu hanyoyin karkashin kasa.

Wannan ya tilasta wasu da suka yi niyyar jefa kuriar da yammacin jiyan rashin samun damar yin hakan, wannan ambaliyar ma ya sa dole an kulle wasu wuraren jefa kuria 2 tun lokaci baiyi ba.

Sai dai kuma wasu jamaan duk da wannan ruwan saman sai da suka kokarta suka tabbatar sun jefa kuriaar domin wannan batu a ganin su, abu ne da ke da nasaba da zaman lafiya wadda akan haka ne aka samar da kungiyar ta tarayyar turai.