Birtaniya: Majalisar Dokoki Ta Yi Watsi Da Kiran Sabon Zabe

A karo na biyu, Majalisar Dokokin Burtaniya ta yi watsi da shirin Firai minista, Boris Johnson, na gudanar da zabe da wuri, a wani yunkuri na ganin ba a saba ma wa’adin ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai ba.

Johnson ya so a goyi bayan aniyarsa ta gudanar da zaben gaggawa ranar 15 ga watan Oktoba, a yunkurinsa na neman samun rinjaye a Majalisar, saboda ta amince da tsarinsa na shirin ficewar, ko Brexit, gabanin babban taron Shugabannin kungiyar ta Tarayyar Turai, EU.

Bayan kuri’ar ta bijirewa da aka kada jiya Litinin, Johnson ya aiwatar da shirin nan na sa da ake takaddama a kai, na dakatar da Majalisar Dokokin na tsawon makonni biyar, har sai Sarauniyar Ingila ta gabatar da jawabinta na shekara- shekara ga majalisar Dokokin, mai kunshe da bayanin shirin ayyukan Majalisar da gwamnati za ta aiwatar a shekara mai zuwa.

Watsi da batun gudanar da wani sabon zabe da Majalisar ta yi, na zuwa ne ‘yan sa’o’i bayan da Sarauniya Elizabeth ta Ingila, ta bayar da goyon bayanta ga kudurin dokar hana Johnson aiwatar da shirinsa na Brexit ba sharadi, wato ficewa daga Tarayyar Turai a ranar 31 ga watan Oktoba, ba tare da an zayyana yarjajeniyar rabuwar ba.