Bincike Ya Nuna Roba Na Taimakawa Wajen Dumamar Yanayi

Irin robobin da suke haddasa dumamar yanayi

Wani binciken da Jami'ar Hawaii ta gudanar ya nuna cewa roba da glashi na kan gaba wajen haddasa dumamar yanayi

Wani binciken da aka gudanar ya nuna cewa roba na taimakawa kwarai wajen dumaman yanayi.

Masana ilmin kimiyya masu rubutu a mujallar nan mai suna PLOS ONE sun fada jiya Laraba cewa leda na fitar da turiri musamman lokacin da hasken rana ya buge ta.

Masanan sun gudanar da binciken su ta hanyar gwaji a kullun akan abubuwan dake da nasaba da roban da ake zuba ruwa ciki, ko kuma ledar da ake sa kayayyakin da aka yi sayayya a kantuna ko kuma wadda aka zuba abinci.

Kamar yadda babban jami’in gudanar da bincike David Karl na Jami’ar Hawaii yake cewa, roba tana a matsayin abinda keda tasiri ga gilashi wanda ake sa ran yana kara dumaman yanayi.

Iskar gas din nan mai launi iri daban-daban da ledan da ake sarrafawa sune kan gaba wajen samar da canjin yanayi