wani tsohon Lauyan Shugaban Amurka Donald Trump ya ce mai bincike na musamman kan katsalandan din Rasha da Rasha ta yi a zaben Shugaban kasar Amurka na 2016 ya nuna da yiwuwar ya yi amfani da doka wajen tilasta Shugaba Trump ya bayar da ba'asi.
John Wowd ya gaya ma Associated Press da kuma Reuters cewa mai bincike na musamman Robert Mueller ya ambaci yiwuwar gabatar da umurnin bayar da ba'asin ga Shugabata Trump, a yayin wata ganawa da tawagar lauyoyinsa a watan Maris. Wannan kalamin na Dowd ya tabbatar da wani labarin da jaridar Washington Post ta wallafa tun farko.
Dowd ya fice daga tawagar ta lauyoyin da ke kare Trump jim kadan bayan da su ka gana da Mueller.
Mueller na binciken gano ko shin kwamitin yakin neman zaben Trump ya hada baki da Rasha wajen yin katsalandan a zaben, da kuma ko shin Trump ya yi yinkurin zagon kasa ma shi kansa binciken.
Trump dai ya sha musanta cewa kwamitin yakin neman zabensa ya hada baki da Rasha wajen yin katsalandan a zaben na 2016, ya na mai kiran binciken da Mueller ke yi 'bi-ta-da-kulli.'