Ana ci gaba da shirye shiryen gudanar da jana’izar zakaran dan damben zamani na Amurka, Muhammad Ali, wanda da ya rasu cikin daren juma’a, yana mai shekaru 74, bayan da ya sha fama da cutar Parkinson mai sa kakkarwa.
WASHINGTON D.C. —
A wani taron manema labarai da aka gudanar a jiya Asabar, wakilan iyalan Muhammad Ali sun bayyana cewa ranar juma’a za a yi jana’izarsa a mahaifarsa da ke birnin Louisville, a jihar Kenturkey.
Ana kuma sa ran tsohon shugaban Amurka, Bill Clinton na daga cikin bakin da za su gabatar da jawaban ban-kwana, baya ga shararren dan wasan barkwanci Billy Crystal da kuma fitaccen mai karanta labarai Bryant Gumbel da suma za su gabatar da nasu jawaban.
Yanzu haka a birnin na Louisville, an rage tsayin totoci tare da gudanar da addu’oi a sassansa domin nuna alhinin rasuwar shararren dan damben.