Biden Zai Iya Yin Galaba Akan Trump a Zabe - Bincike

Dan takarar shugaban Amurka na jam’iyyar Democrat Joe Biden zai yi galaba akan shugaba Donald Trump da babbar tazara idan yau za a gudanar zabe a cewar wani sabon binciken jin ra’ayoyin jama’a.

Sabon binciken wanda Reuters-Ipsos ya tattara, ya nuna cewa kashi 48 cikin 100 na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun ce za su jefa wa Biden kuri’a, kashi 35 cikin 100 kuma suka ce za su jefawa Trump.

Bayan haka kashi 40 cikin 100 na ra’ayoyin sun nuna gamsuwa da yadda Trump ya tunkari annobar coronavirus, kashi 55 kuma suka nuna akasin haka.

Gaba daya, binciken jin ra’ayoyin ya nuna cewa Trump na da farin jini da kashi 38 cikin 100.

Amma akwai albishir ga Trump domin binciken ya kuma nuna cewa kashi 43 cikin 100 na ra’ayoyin sun yi imanin cewa Trump zai fi yin aiki a bangaren tattalin arziki fiye da Biden wanda ya samu kashi 38 cikin 100.