Biden Ya Zabi Mace Bakar Fata A Matsayin Mataimakiyarsa

Mataimakin shugaban kasa Joe Biden da Sanata Kamala Harris

Dan takarar da ake kyautata zaton shi zai tsayawa jam'iyyar Democrat takara a zaben shugaban kasa Joe Biden, ya zabi Sanata Kamala Harris a matsayin abokiyar takararsa, mace ta farko bakar fata- ba'indiya da wata babbar jami'yya ta taba zaba.

"ina farin cikin sanar da cewa na zabi Kamala Harris – jaruma, marar tsoro, kuma daya daga cikin babbar mai bautawa kasar ta - a matsayin mataimakiya ta," a jiya Talata da maraice. "Tare zamu kayar da Trump."

Harris na daga cikin ‘yan jam'iyar Democrats da suka fafata a zaben neman jam'iyyar ta basu tikitin tsaya takarar shugaban kasa, a zaben 2020 mai zuwa, inda Biden ya samu nasara.

Bayan da ya lashen zaben na jam’iyya, Biden ya yi alkawarin zaben mace a matsayin mataimakiyar sa. Akwai jita-jita da yawa, cewa dama zai zabi mace bakar fata da za ta yi takara da shi.

Harris, mai shekaru 55, an haife ta a California, sannan mahaifin ta haifaffen kasar Jamaica ne, mahaifiyarta Ba'Indiya kuma Ba’amurkiya. Ta samu daukaka ne bayan da aka zabe ta babbar lauya a California a shekara 2010, inda ta sami yabo daga masu fafutukar kare hakkin dan adam saboda kin amincewa da karar da aka gabatar akan dokar hana masu auren jinsi daya yin zabe.

Masu fashin baki sun bayyana mabambantan ra'ayoyi a kan daukar da Biden ya yi wa Harris a matsayin mai dafa masa baya a zaben watan Nuwamba. Wasu cewa suke zaben na Harris ba zai yi wani tasiri ba saboda shugaban kasa Amurkawa za su zaba, amma ba mataimaki ba.

Ita kuwa Helen Bako 'yar Najeriya dake zaune a jihar California, jihar Kamala Harris ta asali, ta ce akwai yiwuwar Harris za ta taka rawar gani, lamarin da ka iya kai Democrat ga lashe zaben shugaban kasa.

Bayan da Biden ya zabi Harris a jiya Talata, shugaba Trump ya ce ya yi mamakin cewa ita Biden ya zaba a matsayin mataimakiyar shugaban kasa, inda ya kuma kwatanta yunkurin da ta yi na neman takararar shugaban kasa a matsayin gazawa.

Helen Bako ta bayyana ra'ayin na ta ne a hirar ta da Alheri Grace Abdu:

Your browser doesn’t support HTML5

RA'AYIN HELEN BAKO A KAN HARRIS