Biden Ya Yi Ta’aziyar Mutanen Da Iftila’in Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Najeriya

  • VOA Hausa

Shugaban Najeriya Bola Tinubu da takwararsa na Amurka Joe Biden

Shugaba Joe Biden na Amurka ya jajanta game da iftila’in ambaliyar ruwan baya-bayan nan da ta shafi yankin arewa maso gabashin Najeriya.

A hirarsa ta wayar tarho da Shugaba Bola Tinubu ya jinjinawa salon jagorancin Shugaba Tinubu wajen sakin ba-Amurke kuma tsohon jami’in tsaron Amurka Tigran Gambaryan a bisa dalilai na jin kai.

Shugabannin 2 sun kuma tattauna a kan mahimmancin alakar Najeriya da Amurka wajen shawo kan matsalolin duniya tare da bunkasa tsaro da wanzuwar arziki a bangarori da dama.

Musamman, Shugaban Biden ya bayyana yabawarsa da hadin kai a kan harkokin tsaro, ciki har da sanarwar baya-bayan nan a kan kawancen wasu kasashe wajen yaki da almundahanar kudade da kudin crypto, da hadin kai a kan sabbin fasahohin zamani da kuma ra’ayin bai daya na sauya fasalin hukumomin kasa da kasa su rika sauraron muryoyin kasashen Afirka.

A ranar 15 ga watan Oktoba da ya gabata ne gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi watsi da dukkanin tuhume-tuhume da take yiwa babban jami’in kamfanin Binance, Tigran Gambaryan a bisa dalilai na rashin lafiya.

Ku Duba Wannan Ma Gwamnatin Najeriya Ta Wanke Jami’in Binance Gambaryan Daga Dukkanin Tuhuma
Ku Duba Wannan Ma Gwamnatin Amurka Ta Yi Farin Ciki Da Sakin Jami’in Binance Gambaryan

Gambaryan ya kasance a tsare yana fuskantar shari’a akan halasta kudaden haram tun cikin watan Afrilun da ya gabata.

Lauyan hukumar EFCC, mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati a Najeriya, ne ya sanar da janye tuhume-tuhumen a gaban Mai Shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya dake Abuja.