Tsohon mataimakin shuagabn kasa Joe Biden ya samu gagarumar nasara a zaben fidda gwani da jami’aiyar Democrat ta yi a jihar South Carolina, lamarin da ya sake farfado da kempensa da ya yi rauni da kuma bashi kwarin gwiwan shiga muhimman takara a ranar Talata inda jihohi 14 zasu yi zabe lokaci guda.
WASHINGTON DC —
Bayan rashin kokarinsa a takara uku na zaben fidda gwani a baya, masu fashin baki sun yi hasashen cewa yakin neman zaben Biden ka iya rushewa idan bai yi nasara a zaben na jihar South Carolina ba, inda ya samu gagarumar nasara da kuru’un bakar fatar Amurka ‘yan Democrat masu dimbin yawa a jihar.
Baicin kashi da Biden ya baiwa sanatan Vermon Bernie Sanders, wanda ya shiga takarar a matsayin wanda ke kan gaba cikin ‘yan takaran, ya kuma nuna zai iya fafatawa da shi tare da tabbatarwa masu kada kuri’a cewa Sanders ba zai gagare shi ba.
A cikin sakamakon da ya kai kashi 60 cikin dari, alamu sun nuna Biden ya lashe kashi 50 cikin dari na kuru’un. Shiko Sanders yana baya da kashi 19 cikin dari.