Shugaban hukumar gudanarwa da kasafi na Amurka, Shalanda D. Young ce za ta jagoranci tawagar.
washington dc —
Shugaba Joe Biden na Amurka ya sanar da tawagar shugaban kasa ta musamman da za ta halarci bikin rantsar da Shugaba John Dramani Mahama na Ghana a ranar 7 ga watan Janairun da muke ciki, a birnin Accra, na kasar Ghana.
Shugaban hukumar gudanarwa da kasafi na Amurka, Shalanda D. Young ce za ta jagoranci tawagar.
Mambobin tawagar sun hada da jakadiyar Amurka a kasar Ghana, Virginia E. Palmer da magajin garin Los Angeles na jihar California, Karen Bass, da mashawarcin shugaban kasa na musamman kuma babban darakta akan al’amuran afrika da kwamitin tsaron kasa da kuma fadar White House, Frances Z. Brown.
Ku Duba Wannan Ma Ghana: John Mahama Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa A Hukumance Ku Duba Wannan Ma Bawumia Ya Rungumi Kaddarar Faduwa Zaben Shugaban Kasar Ghana