Tun daga farkon shekarar 2025, Ghana za ta kyale 'yan Afirka daga kowace kasa su shiga kasarta ba tare da neman izinin shiga (biza) ba, sakamakon sahalewar baya-bayan nan da shugaban kasar Nana Akufo-Addo ya yi.
Shugaban kasar ya fara ayyana manufar ne yayin taron tattauna hanyoyin bunkasar Afirka, inda ya bayyana hakan da hanyar yaukaka alaka tsakanin kasashen nahiyar da bunkasa yawon shakatawa da cinikayya da kuma tafiye-tafiye.
Ghana na baiwa al'ummomin kasashen Afirka 26 damar shiga kasarta kyauta tare da baiwa 'yan wasu kasashe 25 izinin shiga kasar bayan da suka isa can, inda 'yan kasashe 2 ne kacal ke bukatar neman biza kafin su shiga
Ta hanyar fadada damar shiga kasar kyauta ba tare da bisa ba ga ilahirin al'ummar nahiyar Afirka, Ghana ta bi sahun kasashen Rwanda, Seychelles, Gambia da Jamhuriyar Benin a jerin kasashen Afirka da ke aiwatar da irin wannan manufar tafiye-tafiye ga kowa.
Dandalin Mu Tattauna