Biden Ya Nemi Majalisa Ta Gaggauta Tabbatar Da Tallafin COVID-19 Don Ceto Tattalin Arzikin Kasar

Zababben shugaban Amurka Joe Biden

Zababben shugaban Amurka Joe Biden ya yi hasashen ganin makoma mai tattare da kalubaloli, idan majalisun kasar basu gaggauta daukar mataki a kan kudirin tallafin coronavirus, yayin da cutar ke kara ta’azzara a fadin kasar, lamarin dake kawo cikas ga farfadowar kasar.

Biden ya bayyana haka ne a jawabin da ya yi jiya Juma’a da rana a kan rahoton watan Nuwamba a kan ayyukan yi, wanda ya nuna daukar ma’aikata a Amurka ya yi kasa ainun yayin da ayyuka miliyan goma kuma suka yi rauni fiye da kafin annobar.

Democrat ta kira rahoton da mai daga hankali kana ta ce hakan na nuni da yanda tattalin arzikin ke tattare da matsaloli, amma Biden ya ce matakin gaggawa da majalisa zata dauka zai takaita matsalolin tattalin arzikin.

Ya ce “idan muka muka dau mataki yanzu, ina nufin yanzu, zamu iya farfadowa kana mu fara gina makoma mai inganci," inji shi. Ya ce babu batun bata lokacin.

Karuwan kamuwa da cutar COVID-19 ya kai jihohi da hukumomin garuruwa ga sauya matakan su na bude harkokin su. Kana akwai yiwuwar kafa dokokin kulle yayin da ake shiga lokacin sanyi da kuma tafiye tafiye a lokacin hutu da ka iya kai ga sabbin kamuwa da cutar da ma sabbin mace mace.

Tun da safiyar jiya Juma’a kakakin majalisar wakilai Nancy Pelosi ta bayyana alamun tabbatar da kudirin tallafin COVID-19 da wani kudirin kashe kudin gwamnati na dala triliyan guda da digo hudu.