Wata tawagar sanatocin majalisar dokokin Amurka, ta gana da gwamnatin shugaba Joe Biden kan tallafin dala triliyan 1.9 da za a samar don rage radadin da annobar covid-19 ta haifar, inda tawagar ta nuna fatan amincewa da dokar gabanin a fara zaman tsige tsohon shugaba Donald Trump.
Sanatocin, wadanda suka hada da na jam’iyyar Democrat da na Republican, sun yi ammanar cewa, abu muhimmi a daidai wannan lokaci shi ne, a hanzarta samar da allurar rigakafi, da kuma kara kaimi wajen gudanar da ayyukan gwajin cutar.
Wasu daga cikin ‘yan Republican sun dasa alamar tambaya, kan dalilin da ya sa za a kashe wadannan makudan kudade, wata guda, bayan da majalisar dokokin Amurka ta amince da tallafin dala biliyan 900.
Tallafin na farko na zuwa ne, bayan da aka yi ta tafka muhawara kan kudaden da za su shiga aljihun Amurkawa.
Matsaya ta karshe da aka cimma ita ce, za a bai wa kowanne mutum daya har zuwa dala 600 – inda kudin zai rika raguwa daidai iya samun mutum.