Beckham Ya Isa Sweden Don Halartar Jana’izar Eriksson

Beckham, dama, marigayi Eriksson, hagu

Beckham ya kasance shi ne kyaftin din Ingila a lokacin da Eriksson yake horar da tawagar kasar inda ya yi aiki daga 2001 zuwa 2006.

Tsohon kyaftin din Ingila David Beckham ya isa kasar Swden don halartar jana’izar Sven-Goran Eriksson, wanda ya taba horar da ‘yan wasan Ingila.

Eriksson ya rasu a ranar 26 ga watan Agusta yana mai shekaru 76.

Ya taba bayyana cewa yana fama da cutar kansa kuma yana da shekara daya da zai rayuwa.

Beckham ya kasance shi ne kyaftin din Ingila a lokacin da Eriksson yake horar da tawagar kasar inda ya yi aiki daga 2001 zuwa 2006.

A watan Yuni Backham ya kai wa Eriksson ziyarar.

Kamfanin Dillancin labaraina Sweden TT ya ce a daren Alhamis Beckham ya sauka a filin tashin jirage na Karlstad.