Bazoum Ya Cika Watanni Uku A Hannun Sojojin Da Suka Yi Juyin Mulki A Nijar

Mohamed Bazoum

Hambararren shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum ya cika watanni uku a tsare tare da mai dakinsa da dansa, tun bayan da sojoji suka kifar da gwamnatinsa a ranar 26 ga watan Yuli, lamarin da ya sa har yanzu makomarsa ke cikin rashin tabbas.

A ranar 26 ga watan Yulin wannan shekarar ne, wato watanni uku kenan sojoji suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar a fadar shugaban kasar da ke babban birnin Yamai, inda jami’in sojoji Abdurahamane Tchiani ya samu kansa a matsayin mai jan akalar kasar bayan hambarar da shugaban Nijar Mohamed Bazoum wanda yanzu haka ake cigaba da tsare da shi tare da matarsa a gidansa da ke fadar shugaban kasa.

Tuni al'ummar kasar ta Nijar suka soma bayyana ra'ayoyinsu akan watanni uku da juyin mulki a nijar.

A ra'ayin wasu al’ummar kasar Nijar dai wannan ya kasance mafarin samun ci gaban kasar yayin da wasu kuma ke ganin sa a matsayin mafarin shigar su cikin hali na rashin tabbas.

Masu fashin baki kan al’amurran yau da kullun irinsu Abdurahamane Dikko na ganin watanni uku da juyin mulki an samu wasu nasarori.

A halin yanzu, shugabannin mulkin sojoji a Nijar na ci gaba da neman hanyoyin daidaita al’ammurra, musamman gamsar da kungiyar ECOWAS na amincewa da kudirinsu domin sassauta wasu daga cikin takunkuman da aka kakabawa kasar ta Nijar.

Saurari rahoton Hamid Mahmud :

Your browser doesn’t support HTML5

Bazoum Ya Cika Watanni Uku A Hannun Sojojin Da Suka Yi Juyin Mulki A Nijar