Ministan cikin gida a Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohamed ya ajiye aikinsa domin fara shirin tunkarar zaben shugaban kasa.
Matakin na zuwa ne yayin wata kwarya-kwaryar garambawul din da Shugaba Issouhou Mahamadou ya yi wa gwamnatinsa a ranar Litinin da daddare.
A hirarsu da Souley Moumouni Barma a Yamai kakakin jam’iyyar PNDS Tarayya mai mulki, Alhaji Assoumana Mahamadou ya ce matakin zai bai wa dan takararsu damar maida hankali wajen shirye-shiryen zaben watan Disambar da ke tafe.
“Mu a matsayinmu na PDNS Tarayya, wannan abu da aka yi mun karbe shi da hannun bibiyu, domin zai ba shi dama ya gana da mabiya bayan jam’iyya.” In ji Mahamadou.
Ya kara da cewa, “lokacin da yake ministan cikin gida ba ma samun damar mu gana da shi a kowane lokaci.”
A cewar Kakakin jam’iyyar, shi Bazoum ne da kansa ya nemi shugaba Issouhou da ya sallame shi.
“Mun gode ma shi ma minista na cikin gida wanda ya nemi a sallame she saboda ya je ya yi wa jam’iyya aiki kamar yadda muke bukata.”
Dangane da tambayar ko an samu baraka ne a tsakanin jam’iyyar ta PNDS, kakakin jam’iyyar Mahamadou ya ce ba haka lamarin yake ba.
“Jam’iyyar PDNS Tarayya ba a batun rarrabuwar kawuna, mu ba mu san wannan batu ba.”
Saurari cikakkiyar hirar Souley Moumouni Barma da Assoumana Mahamadou:
Your browser doesn’t support HTML5