Sa’oi kadan bayan da kotun tsarin mulkin kasar ta tabbatar da su, jam’iyyun siyasa suka fara ba da sanarwa game da wanda suke fatan magoya bayansu su bai wa kuri’a a tsakanin dan takarar adawa da na jam’iya mai mulki.
Cibiyar jam’iyyar ANDP Zaman lafiya a yammacin ranar Lahadi magoya bayan ta suka yi gangamin goyon bayan dan takarar jam’iyar PNDS Tarayya Bazoum Mohamed a matsayin wanda suke fatan ya lashe zagaye a zaben, saboda abin da suka kira kyakkyawar alaka da ke tsakanin wadannan jam’iyyu.
Dan takarar ANDP Moussa Baraje na daga cikin wadanda suka taka rawar gani a zagayen farko na zaben shugaban kasa dalilin da ya sa kenan jam’iyar ke kiran ‘yayanta su fito a ranar 21 ga watan Fabrairu don yiwa Bazoum Mohamed kara.
Jam’iyu akalla 3 ne suka bayyana goyon baya ga dan takarar jam’iya mai mulki a tsawon wunin jiya Lahdi cikinsu har da RPP Farilla ta Alma Oumarou.
Ko ya ‘yan hamayya ke kallon wannan al’amari? Tambayar kenan da wakilin Muryar Amurka ya yi wa Bana Ibrahim mamba a kwamitin yakin zaben dan takarar RDR Canji Mahaman Ousman.
"Babu fargaba, babu abin da ya ta da mana hankali, aiki ne muke yi tukuru domin mu tunkari zabukan nan. Kama inch Allah, za mu zagaya Kasa mu kai must salon Mahamane Ousmane." In ji Bana.
A 12 daren jiya aka kaddamar da yakin zabe a hukunce saboda haka mukarraban ‘yan takarar da za su je zagaye na biyu na wannan zabe kowanne ana su bangare suka fara haramar zagaya sassan kasa da nufin bajewa talakawa manufofin siyasar da suke sa ran shimfidawa idan aka ba su yarda a lokacin zaben
A saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma daga Yamai:
Your browser doesn’t support HTML5