Kungiyar kwallon kafar Bayern Munic ta kasar Jamus ta lashe gasar zakarun Turai ta bana, bayan da ta doke PSG ta kasar Faransa da ci 1-0 a wasan karshe ta gasar da aka buga a Lisbon.
Wannan ya jaddada nasarar Bayern din a wannan kakar wasannin na lashe gasar karo na 6 a tarihi, bayan da kuma ta lashe babbar gasar Bundesliga ta kasar Jamus da kuma kofin kalubalen ka na Jamus.
Wasan na karshe yayi zafin gaske, inda kungiyoyin 2 suka yi ta kai wa juna farmaki, inda daga karshe dan wasan Bayern din Kingsley Coman ya sami zura kwallon da ka a minti na 59 na wasan, wanda ya baiwa kungiyar nasara.
PSG ko ta yi ta yunkuri tare da kai farmaki, inda kiris ya rage ‘yan wasanta 3; Neymar, Kylian Mbappe da Angel Di Maria su zura kwallon a lokuta daban-daban, to amma kuma haka ba ta cimma ruwa ba.