A rahotannin da mu ke kawo muku na watan Ramadana, a yau dandalin VOA ya samu bakuncin Mallam, Isma’il Ahmad Isma’il, wanda ya yi mana tsokaci dangane da mutanen da ya kamata su azumci watan Ramadana.
Ya ce Allah ya wajabta azumi ga mutanen yanzu kamar yadda ya wajabta wa mutanen da su ka gabata, saboda su ma mutanen yanzu su samu taqawa.
Da ya ke bayyana wadanda azumi ya hau kansu, ya ce da farko akwai mumini Musulmi saboda azumi bai halatta ga wanda ba mumini ba.
Na biyu shi ne baligi wato mai iya banbanta ayyukan lada da kuma na zunubi. Na uku kuma shi ne wanda ya rayu har zuwa loacin azumun watan Ramadan. Na hudu kuma wanda ya mallaki hankalin kansa.
Sheikh Isma’il ya ce wadanda azumin bai wajaba gare su a halin yanzu ba, sun karkasu: Akwai wadanda ramakon azumi ya wajaba kansu da kuma wadanda ramako bai wajaba kansu ba – sai dai su ciyar.
Bayan da ya ja aya, sai Sheikh Isma’il ya ce da matafiyi da marar lafiya da kuma mace mai haila da mace mai ciki duk ba za su yi azumi ba sai daga baya su yi ramko.
Sannan sai Sheikh ya sake jan aya ya ce wadanda su ke da rauni ko wani irin nakasu – kamar tsoffi da wadanda ba za su iya jure yunwa ba saboda ciwo irin ulsa ko sikila da ba za su iya azumi ba, sai su ciyar da miskinai.
Ga wakiliyarmu Baraka Bashir da cikakken bayanin Sheikh Isma’il:
Your browser doesn’t support HTML5