Fatima Aliyu Tanko - matashiya mai harkar kayan daki kama daga gadaje da kujeru na amare wadanda take kawowa daga kasashen wajen, inda ta bude shago na wannan sana’ar tata, kimanin shekaru biyu da suka wuce.
Ta ce tun tana jami’a ne ake yawan neman shawarta na yadda za’a gyarawa amare ko sabon gida, hakan ne ya sa ta ga me zai hana ta bude harkar kayan daki, domin baiwa mutane shawara kuma ta fara wannan sana’a shekaru biyu da suka wuce.
Ta ce bashi ya zama tamkar kalubale ga duk wani mai sana’a, sai dai dole idan zai yi sana’a sai mutum ya fuskanci wannan matsalar, dole sai da juriya da kau da kai.
Fatima ta ce kafin ta fara harkar kasuwanci gadaje da kujeru sai da ta nemi shawa’awar wadanda suke ire-iren wadannan harka, domin samun fahimta na yadda ake harkar shigo da irin wadannan kayayyakin, ko da yake a wannan lokaci bata da isasun kudaden da zata bude shago na kashin kanta, maimakon haka sai ta sanya hannun jari a sana’ar daga wajen kawunta.
Babban burinta dai ta ce bai wuce ta zama Interior Decorator wato mai kawata gidaje da za’a dinga baiwa mutane shawarar yadda zasu kawata gidajensu, ta kuma bude babban waje da zata kawata shi yadda ta ke so na harkar kayan gidaje.
Your browser doesn’t support HTML5