Bawumia Ya Rungumi Kaddarar Faduwa Zaben Shugaban Kasar Ghana

Mahamadu Bawumia

Bawumia ya kuma taya abokin hamayyarrsa John Dramani Mahama murnar nasarar lashe zaben da aka gudanar a ranar 7 ga watan Disamban 2024.

Maitaimakin shugaban kasa kuma dan takaran shugaban kasa a karakashin jamiyar NPP mai mulki, Mahmudu Bawumia ya amince da shan kaye a zaben shugban kasa.

Bawumia ya kuma taya abokin hamayyarrsa John Dramani Mahama murnar nasarar lashe zaben da aka gudanar a ranar 7 ga watan Disamban 2024.

Yayin jawabi da manema labarai, Bawumia yace ya kira tsohon shugaban kasa John Dramani Mahama, kuma ya taya shi murnar samun nasara a zaben bana.

Bawumiya ya bayyana cewa “al’umar Ghana sun bayyana abin dake zuciyarsu bisa sauyi da suke buketa don haka na yi mubayi’a”

Dan takarar jam'iyyar NDC mai adawa kuma tsohon shugaban kasar Ghana, John Mahama a shafinsa na X ya amsa tayar murnar da Bawumiya ya yi masa nan take.