Kwamishinan ‘yan sandan jahar Bauchi, Mohammed Zaki Ahmed, ya tabbatar da cewa cikin mutanen da suka damke akwai ‘yan fashi da makami da kuma wasu masu garkuwa da mutane. Ya kuma ‘kara da cewa jakadan masu garkuwa da mutane da suka kama yana nan yana taimaka musu wajen samun bayanai.
Haka kuma bayanai daga hukumar ‘yan sandan jahar Gombe na cewa an samu karuwar yawan mutanen da suka rasa rayukansu a sanadiyar motar nan da ta afkawa ‘dalibai masu bikin Maulidi a garin Mallam Sidi dake karamar hukumar Kwami a jahar Gombe.
A baya dai jami’in hukumar ‘yan sandan jahar Gombe, Ahmed Usman, ya bayar da jimlar mutane takwas da suka rasa rayukansu, amma ya zuwa yau Alhamis jimlar ta ‘karu inda sama da mutane 12 ne suka rasu.
Kakakin hukumar ‘yan sandan jahar Gombe DSP Ahmed Usman, yace hukumar ta yi aiki wajen ganin ta kwantar da tarzomar da ta faru biyo bayan hatsarin, haka kuma ta hukumar ta mika alhininta ga iyayen wadanda suka rasa rayukansu, kuma ana nan ana ci gaba da gudanar da bincike.
Domin karin bayani saurari rahotan Abdulwahab Muhammad.
Your browser doesn’t support HTML5