Yawancin masu cecekucen suna ganin a daidai wannan lokacin za'a karawa matafiya wahaloli ne kawai.
Saidai ministan sufurin jiragen sama na Najeriya yayi karin haske akan wannan shirin na rufe filin na tsawon makonni shida kawai.
Ministan Alhaji Hadi Sirika yace gyaran tilas ne a yishi domin a kaucewa hadari. Daben da aka yi na saukan jiragen an yishi ne ya kai shekaru 25 bayan nan a sake yin wani. Yace a birni irin Abuja ya kamata a ce akwai daben biyu.
Lokacin da aka gina filin ana sa zato fasinjoji ba zasu wuce dubu dari ba a shekara amma bayan gwamnatin tarayya ta dawo Abuja yanzu ana samun mutane miliyan takwas kowace shekara. Sauka da tashi suka karu biye da tsammani.
Yanzu daben ya kai shekaru 35 mai makon 25, wato ya kara shekaru goma, wanda ya wuce lokacin da yakamata a sake ginashi. Dalili ke nan da ya sa yana ballewa ana samun ramuka a tsakitarshi.
Wani matukin jirgin sama kuma kwararre a harkokin jiragen sama yace babu makawa tilas ne gwamnati ta dauki wannan matakin.
Ga rahoton Umar Faaruk Musa da karin bayani.