BAUCHI: Majalisar Dokokin Jihar Ta Zabi Sabon Kakakin Majalisa Da Mataimakinsa

Majalisar Dokoki a daya daga cikin jihohin Najeriya

'Yan majalisar dokokin jihar Bauchi sun zabi sabon kakakin majalisa da mataimakinsa bayan da kotun daukaka kara ta tsige tsohon kakakin majalisar Abubakar Suleiman da mataimakinsa Jamilu Barade a ranar Laraba.

Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta soke zaɓen Abubakar Sulaiman saboda a cewarta yana cike da kura-kurai inda ta bayar da umarnin a sake zaɓe a rumfuna 10 na mazaɓar Ningi.

Yan majalisar sun zaɓi ɗan majalisar da ke wakiltar mazaɓar Hardawa, Babayo Muhammad a matsayin sabon kakakin majalisar.

Hakazalika, sun kuma zaɓi ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Dass, Ahmad Abdullahi, a matsayin mataimakin kakakin majalisar.

Kotun daukaka ƙara da ke zamanta a Abuja, a wani hukunci da ta yanke, ta soke zaɓen mataimakin kakakin majalisar, Jamilu Umarau Dahiru, mai wakiltar mazaɓar Bauchi ta Tsakiya.

Za a sake gudanar da zaɓe a wasu rumfunan zaɓe na mazabun tsohon kakakin majalisar da mataimakinsa domin tantance waɗanda suka lashe lashe zaɓen.

A halin yanzu, Gwamnan Jihar Bala Mohammed, zai gabatar da kudirin kasafin kudin jihar na shekarar 2024 ga majalisar a ranar Alhamis.